Podcasts by Category

Al'adun Gargajiya

Al'adun Gargajiya

RFI Hausa

Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam.  Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.

321 - Yadda tsadar rayuwa ke barzana ga Maroka da Sankira a Jamhuriyar Nijar
0:00 / 0:00
1x
  • 321 - Yadda tsadar rayuwa ke barzana ga Maroka da Sankira a Jamhuriyar Nijar

    Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ya duba yadda jama'a a Maradi suka koma amfani da ruwan randa a maimakon kankara lokacin azumin watan Ramadana, saboda tsadar kankarar.

    Akwai mu dauke da yadda Maroka da kuma Sankira ke fuskantar barazana a sakamakon tsadar rayuwa.

    Dannan alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Abdullahi Isa.

    Tue, 26 Mar 2024
  • 320 - Yadda masarautar Hausawan Turai ke gudanar da ayyukanta

    Shirin Al'adun Gargajiya na wannan makon ya ziyarci masarautar Sarkin Hausan Turai Alhaji Surajo Jankado Labbo da ke kasar Faransa, inda Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da shi kan wasu batutuwa da suka shafi Hausawa. 

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa........

    Tue, 19 Mar 2024
  • 319 - Tasirin masu sarautar gargajiya wajen inganta tsaro a yankunansu

    A sakamakon gyaran da aka yi wa kundin tsarin mulkin Nigeria na 1976,  aka tsame hannun sarakunan gargajiya a kasar cikin sha’anin kula da harkokin tsaro da harkokin shari’ah  da kuma batun tara haraji a cikin al’ummarsu.
    Hakan ne ya sanya Sarakuna duk da kasancewarsu iyayen kasa, suka koma gefe inda suka zamo ‘yan kallo kan wadannan al’amura.
     

    Amma yayinda gwamnatin Nigeria ke tunanin sake damka wa Sarakuna wannan dama, wasu daga cikin su fara bijiro da sabbin matakai da nufin tsare rayuka da dukiyar al’ummarsu daga ‘yan ta’adda.

    A baya bayan nan, Mai Martaba Sarkin Ningi a jihar Bauchi, Alhaji Yunusa Muhammad ‘Danyaya, ya samar da wata katafariyar kungiyar tsaro ta ‘yan sa-kai, wacce ke karade sako da lungun yankin don yaki da miyagun iri.

    Tue, 05 Mar 2024
  • 318 - Yadda kananan kabilu suka samu wakilci a masarautar Katsinar Maradi

    Shirin Al'adun Gargajiya na wannan makon ya ziyarci masarautar Katsina Maradi da ke Jamhuriyar Nijar, inda Sultan Ahmed Ali Zaki ya fitar da wani tsari na nada kananan kabilu a mukaman wakilan al’ummarsu, don kara dankon zumunci tsakanin kabilu sannan da raya al’adun gargajiya a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.Baya ga Fulani da Bugaje da ke zama 'yan gida, Sultan ya nada wakilan Adarawa, Zabarmawa da Tubawa.
     

    Masarautar Katsinar Maradi dai yanzu ta zama madubi kuma abin koyi  a bangaren hadin kan al'ummar Nijar.

    Tue, 27 Feb 2024
  • 317 - Shiri na musamman kan marigayi Salissou Hamissou

    Shirin "Al'adunmu na gado" a wannan makon na musamman ne, wanda ya yi duba akan irin gudunmuwar da marigayi Salissou Hamissou ya bayar a bangaren al'adu, musamman a lokacin da ya ke gabatar da wannan shiri na Al'adunmu na gado. 

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.....

    Tue, 20 Feb 2024
Show More Episodes