Filtrar por género
Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-daban na duniya, tare da nazari kan irin ci gaban da aka samu wajen binciken kimiya da fasaha da ke neman saukakawa Dan’adam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin irin bincike da masana ke yi domin inganta rayuwar Bil’adama. Shirin na zo maku ne, a duk ranar Talata a shirye-shiryenmu na safe, a ku maimata ranar Alhamis.
- 360 - Yadda matasa ke dukufa wajen amfani da Internet don dogaro da kaiTue, 07 May 2024
- 359 - Karuwar masu mallakar takardun kammala karatu na bogi a Najeriya, na barazana ga karewar kwararru
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako ya duba yadda mallakar takardun kammala karatu na bogi a Najeriya ke barzana ga karewar kwararru a fannoni da dama.
Ana fargabar idan har wannan dabi'a ta ci gaba a haka, tabbas za'a rasa kwararru musamman a fannin lafiya, kimiyya da sauransu.
Danna Alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.
Tue, 26 Mar 2024 - 358 - An samar da cibiyar sadarwa a jahar Bauchi don saukakawa dalibai wajen bincike
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan lokacin ya yi duba ne kan yadda wasu kungiyoyi karkashin cibiyar fasahar sadarwa da ci gaban al’umma wato CITAD suka samar da wata katafariyar cibiyar sadarwa da aka yiwa lakabi da HELLO HOPE a jahar Bauchi. Shirin ya kasance wani bangare na yunkurin saukakawa mazauna karkara hanyoyin samun sadarwa ta internet musamman wuraren da babu irin wannan ci gaba ko kuma wuraren da suke da shi amma bashi da karfi, wanda jama’are ke cikin wannan rukuni.
Kungiyoyin da sun sha alwashin samar da irin wannan cibiyar sadarwa guda 20 a shiyoyin Najeriya shida zuwa karshen wannan shekara domin samar da internet a yankunan karkara.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna........
Tue, 19 Mar 2024 - 357 - Taro kan gudummawar kafafen yada labarai a bangaren tsaro a jami'ar ABU Zaria
Matsalar tsaro na daya daga cikin matsalolin da ke addabar Najeriya, musamman ma arewacin kasar, hakan ya sanya sashen koyon aikin jarida na jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria da ke jihar Kaduna ya shirya wani taro gagarumin taro na kasa da kasa domin tattaunawa a kan gudumawar da kafafen yada labarai za su iya bayarwa wajen warware matsalar tsaro. Ya yi wannan ne da zummar taimaka wa kokarin da al'umma ke yi wajen warware wa kansu matsalar tsaron da ke damun su.
Tue, 05 Mar 2024 - 356 - Yadda dalibai ke barin karatu a Nijar don tafiya neman kudi a wasu kasashe
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan lokacin ya yi duba ne kan yadda dalibai da dama a Jamhuriyar Nijar, musaman maza ke barin karatu da sunan tafiya neman kudi, kasashen ketare kamar Libiya, Aljeriya ko kuma hako zinare a kasar Mali kai harma da kokarin tsallakawa Turai, abin da ya sanya kungiyoyin dalibai a kasar bazama aikin wayar da kan matasa kan sanin muhimmancin da ilimi ke da shi.
A Nijar kashi 25 na yara ne ke samun zuwa makarantar boko, kuma daga yara 100 da ake sanyawa a makarantun firamare uku kadai ke kaiwa matakin jami’a.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna........
Tue, 27 Feb 2024 - 355 - Yadda gwamnatin jahar Neja ta fara horas da dalibai sana'oin dogaro da kai
Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan makon zai yi duba ne kan yadda gwamnatin jahar Neja da ke Arewacin Najeriya, ta samar da shirin horas da dalibai sana'oin hannu don dogaro da kai. Gwamnatin jahar dai ta ware ranar Juma'ar kowane mako don gudanar da darasin koyon sana'oin hannu.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna........
Tue, 20 Feb 2024 - 354 - Yadda amfani da komfuta ya shafi kyaun rubutun dalibai
A wannan makon zamu duba yadda ci gaban kimiyya da Ilimi ke zama wani nau’I na koma baya musamman a tsakanin dalibai a Najeriya.
Tun bayan samar ko kuma kirkirar na’urar kwamfuta a 1837, da kuma shigowar ta Najeriya karon farko a 1963 sannu a hankali take bazuwa tsakanin jama’a, yayi da kuma ake samun ci gaba ta fannin amfani da ita.
Wed, 31 Jan 2024 - 353 - Gwamnatin Neja na shirin farfado da tsarin karatun makiyaya
Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan makon zai yi duba ne da tsarin karatun 'yayan makiyaya, wato Nomadic Education. Gwamnatin jihar Neja ce ta yi hobbasa don farfado da shirin karatun 'yayan makiyaya a jihar. Shirin zai bai wa makiyaya damar samun ilimi a duk inda suka yi balaguro don inganta makomarsu. Yanzu haka dai shirye-shirye sun yyi nisa a game dfdaa wannan shirin a jihar Neja mai fara da matsalar tsaro sakamakon ayyukan 'yan bindiga da ke kashe mutane da satar su don kudin fansa.
Tue, 19 Dec 2023 - 352 - Taimakon da kirkirarren Tabarau ke bai wa masu fama da matsalar raunin gani
Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan makon tare da Shamsiyya Haruna ya maida hankali ne kan nazarin da masana kimiya suka yi wajen kirkirar Tabaraun hangen nesa, don taimakawa masu raunin gani. A jamhuriyar Nijar, matsalar gani na zama babban kalubale ga al'ummar kasar wacce a yanzu har aka fara samunta a tsakanin matasa.
Tuni dai matsalar ta sanya likitoci fara kiraye-kiraye ga al'umma da su tashi tsaye wajen kula da lafiyar idonsu.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin......
Tue, 28 Nov 2023 - 351 - Iyayen dalibai a Nijar na kokawa kan tsadar kudin karatuTue, 14 Nov 2023
- 350 - Najeriya: Yadda tsadar man fetur ke ci gaba da yin tasiri kan harkar ilimi
Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan mako tare da Shamsiyya Haruna ya maida hankali ne kan yadda matsalar tsadar man fetur ke ci gaba da yin tasiri akan harkar ilimi a Najeriya, wanda tun bayan sanar da janye tallafin mai a kasar kanana da manyan makarantu ke daukan matakai daban daban da zummar daidaita harkokinsu a cikin wannan yanayi.
Daga cikin wadannan matakai, wasu manyan makarantun musamman jami'o'i sun takaita ranakun zuwan aikin malamai tare da tsawaita lokutan darrusan dalibai.
Tue, 31 Oct 2023 - 349 - Yadda za'a karfafa ilimin fasaha a NajeriyaTue, 24 Oct 2023
- 348 - Tsarin koyar da ilimin Computer ga daliban da ke shirin shiga jami'a a Nijar
Shirin Ilimi hasken rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan tasirin ilimin fasahar na'ura mai kwakwalwa ko kuma computer ga daliban da ke shirin shiga jami'a a Jamhuriyyar Nijar, sabon tsarin da aka bijiro da shi da nufin taimakawa tarin daliban da basu da gogewa a fannin na fasahar na'urar computer.
Wannan mataki dai na da nasaba da yadda ake samun tarin dalibai da basu da cikakkiyar gogewa a fannin na ilimin fasahar na'urar Computer, lamarin da ke zama tarnaki ga tsarin koyo da koyarwar zamani da komi ke shirin komawa tsarin amfani da na'urar ta computer.
Ku latsa alamar sauti don saurarin cikakken shirin...................
Tue, 10 Oct 2023 - 347 - Gudunmowar ilimin sararin samaniya ga ci gaban duniyaTue, 12 Sep 2023
- 346 - Yadda dalibai ke gaza cin jarabawa ta komfuta
Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan mako ya yi duba ne da yada dalibai ke faduwa a jarabawar da ake yi da na'urar komfuta, wato CBT exams. Dallibai dai na yawan kokawa a kaan yadda sukaa faduwa sosai a irin wannan jarabawa, sabanin wadda suka saba, ta alkalami da takarda. Hasali ma daliban naa gaanin cewa matsalar ba daga gare su take ba, inda suka kawo dalilai da dama da ke nnuna cewa ba su daa laifi don sun fadi irin wannan jarabawar.
Tue, 15 Aug 2023 - 345 - Taron kungiyar malaman jaami'o'in shiyyar arewa maso yammacin Najeriya
Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan makon ya mayar da hankali ne kan taron kungiyar malaman jami'o'in shiyyar arewa maso yammacin Najeriya. Makasudin wannan taro kamar yadda kungiyar ta bayyana shine nazari kan irin ci gaban da aka samu ko akasinsa a jam'i'o'in shiyyar da zummar lalubo hanyoyin samun mafita.
Tue, 01 Aug 2023 - 344 - Hanyoyin da ya kamata a bi wajen yaki da barayin waya a NajeriyaTue, 11 Jul 2023
- 343 - Yadda cire tallafin mai a ya shafi harkar ilimi a Najeriya
Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' ya yi nazarari ne kan cire tallafin mai da sabuwar gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu ta yi, inda a lokacin da ya ke gabatar da jawabi jim kadan bayan rantsar da shi, Tinubu ya sanar da janye biyan kudin tallafin mai da gwamnatin kasar ke yi, lamarin da ya sa farashin makamashin ya yi tashin gwauron zabi, kuma ya haifar da karin matsin rayuwa a kasar musamman a bangaren marasa karfi.
Iyaye da daliban abin ya shafe su, ganin yadda matakin ya tilasta wasu iyaye fara tunanin sauyawa 'ya'yansu makaranta sabida kasa iya ci gaba da biyan kudin motar da ake kai su makaranta don neman ilimi, a dayan bangaren ma, al'amarin ya shafi su kansu malaman makartu tun daga matakin Firamari da Sakandari da ma manyan makarantu.
Ku latsa alamar sauti donjin cikakken shirin..........
Tue, 27 Jun 2023 - 342 - Tasirin fasahar AI da ke aron basirar dan Adam ga na'urori a fannin Ilimi
Shirin wannan mako dai ya yi nazari ne kan fasahar nan ta na'urar da ake sanya wa tunanin dan adam wato Artificial Intelligence, wadda a yanzu hankalin kasashen duniya ya fi karkata akai ganin yadda ya zo da gagarumin sauyi mai ban mamaki.
Sai dai duk da ci gaban da wannan fasahar ta zo da shi da ma wanda ake hasashen za ta samar nan da shekaru kadan masu zuwa, hankalin kasashen duniya ya rabu gida biyu wurin ci gaba da amincewa da wannan fasaha.
Wed, 14 Jun 2023 - 341 - Tasirin tsarin koyarwa ta yanar gizo ko kuma E-Learning ga daliban Najeriya- 2Tue, 06 Jun 2023
- 340 - Tasirin tsarin koyarwa ta yanar gizo ko kuma E-Learning ga daliban Najeriya
Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna ya mayar da hankali kan tsarin ilimi ta yanar gizo ko kuma na shafukan Intanet da ake kira da E-Learning ko kuma Digilal Learning.
Tun bayan bullar cutar covid-19 ne dalibai da dama suka koma karatu ta yanar gizo ko kuma E-Learning a wani yunkuri na kaucewa ganin karatunsu bai gamu da tangarda ba.
A cikin wannan shirin za ku ji tasirin irin wannan karatu da kuma tagomashin sa ga daliban Najeriya.
Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin...........
Tue, 30 May 2023 - 339 - Ilimi Hasken Rayuwa, na magana kan halin da karatun yara yan gudun hijira ke ciki a NijerTue, 23 May 2023
- 338 - Karancin dakunan karatu na barazana ga karatun Firamare a Neja
Shirin Ilimi hasken rayuwa tare da Shamsiyya Haruna ya mayar da hankali kan kalubalen da karatun Firamare ke fuskanta a jihar Neja ta tsakiyar Najeriya, dai dai lokacin da ake samu karuwar yaran da ke zuwa makaranta.
Mahukuntan jihar Neja sun bayyana cewa adadin daliban da ke shiga Firamare a Neja ya karu daga yara dubu 600 zuwa dubu 800 a bana, sai dai matsalar karancin ajujuwa da kayakin karatun na matsayin babban koma baya ga bangaren ilimi na jihar.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin..............
Tue, 16 May 2023 - 337 - Ko yaya makomar karatun daliban da aka kwashe daga Sudan take?
Shirin na wannan rana, ya duba halin da karatun daliban da suke tsere daga Sudan ke ciki, yayin da rikici ya barke a kasar da ke gabashin Afirka.
Najeriya na daga cikin kasashen da ssuka kwashe dalibai da kuma 'yan kasashen su da ke rayuwa a Sudan, yayin da aka wayi gari da karar harbin bindiga da kuma hare-hare ta sama.
Kasar Sudan dai ta fada cikin rudani tun bayan da rikicin mulki ya barke tsakanin dakarun da ke biyayya ga babban hafsan soji Abdel Fattah al-Burhan da kuma tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo, wanda ke jagorantar rundunar kai daukin gaggaa ta Rapid Support Forces.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin da Shamsiyya Haruna ta gabatar.
Tue, 09 May 2023
Podcasts similares a Ilimi Hasken Rayuwa
- Global News Podcast BBC World Service
- El Partidazo de COPE COPE
- Herrera en COPE COPE
- The Dan Bongino Show Cumulus Podcast Network | Dan Bongino
- Es la Mañana de Federico esRadio
- La Noche de Dieter esRadio
- Hondelatte Raconte - Christophe Hondelatte Europe 1
- Dateline NBC NBC News
- 財經一路發 News98
- La rosa de los vientos OndaCero
- Más de uno OndaCero
- La Zanzara Radio 24
- L'Heure Du Crime RTL
- El Larguero SER Podcast
- Nadie Sabe Nada SER Podcast
- SER Historia SER Podcast
- Todo Concostrina SER Podcast
- 安住紳一郎の日曜天国 TBS RADIO
- アンガールズのジャンピン[オールナイトニッポンPODCAST] ニッポン放送
- 辛坊治郎 ズーム そこまで言うか! ニッポン放送
- 飯田浩司のOK! Cozy up! Podcast ニッポン放送
- 吳淡如人生實用商學院 吳淡如
- 武田鉄矢・今朝の三枚おろし 文化放送PodcastQR
Otros podcasts de Educación
- Franck Ferrand raconte... Radio Classique
- Entrez dans l'Histoire RTL
- Au Cœur de l'Histoire - Des récits pour découvrir et apprendre l'Histoire Europe 1
- Les Cours du Collège de France France Culture
- Choses à Savoir Choses à Savoir
- Historiquement vôtre - Stéphane Bern Europe 1
- 6 Minute English BBC Radio
- Choses à Savoir HISTOIRE Choses à Savoir
- Les récits de Stéphane Bern Europe 1
- Quelle Histoire Quelle Histoire
- Histoire criminelle, les enquêtes de Scotland Yard RTBF
- TED Talks Daily TED
- Histoire des Gangsters Profession Gangster
- Change ma vie : Outils pour l'esprit Clotilde Dusoulier
- L'univers paranormal de Christian Page C23
- La Belle Histoire de France CNEWS
- Parler anglais Choses à Savoir
- Allez j'ose ! Martange
- Nota Bene Benjamin Brillaud
- LA PETITE HISTOIRE La Fabrik Audio