Filtrar por gênero

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau

Muhammad Auwal Sulaiman, Muslim Muhammad Yusuf, Nana Khadija Ibrahim

Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.

578 - Yadda Za Ka Ɗauki Mataki Idan Aka Ɓata Maka Suna Saboda Cin Bashi
0:00 / 0:00
1x
  • 578 - Yadda Za Ka Ɗauki Mataki Idan Aka Ɓata Maka Suna Saboda Cin Bashi

    A wannan zamani da mutum zai iya samun bashi kaitsaye ta waya daga manhajoji daban-daban amma idan mutum ya kasa biya kamfanonin bada bashin kan aika sakonnin cin zarafi da barazana har ga ‘yan uwan wanda ya ci.

    Duk da gargadin da hukumomi mutane da dama na kukan ana ɓata musu suna, kuma an kasa kulle irin wadannan manhajoji kamar yadda aka ce.

    Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan lamarin, da kuma matakin da mutum zai iya dauka idan kamfanin cin bashi suka bata masa suna.

    Fri, 17 May 2024
  • 577 - Abin Da Gwamnati Ke Nufi Da Iya Ƙwazonka, Iya Albashinka

    Gwamnatin tarayyar ta ce za a ɓullo da tsarin auna ƙwazon ma’aikata bisa mizani ta yadda dagewar ma’aikaci zai sa ya samu ƙarin girma ko albashin ma zai iya bambanta, wato dai iya kwazonka iya albashinka.

    Irin wannan yunkuri na gwamnatin tuni ma’aikata da ‘yan kwadago suka fara suka da tunanin wata manufa ce ta kauda hankali.

    Toh ko ta fannin shari’a hakan na da tasiri wajen hakkin ma’aikata?  Shirin Najeriya a Yau ya tattauana kan wannan batu.



    Thu, 16 May 2024
  • 576 - Abin Da Ya Sa Masu Gidajen Haya Suke Tsuga Kuɗi

    A baya-bayan nan mazauna manyan biranen Najeriya na ta kokawa game da yadda masu gidajen haya ke neman mai da su saniyar tatsa  wajen tsuga kudin haya.

    Sai dai masu gidajen na cewa ana fama da tsadar rayuwa kuma kula da irin wadannan gidaje na cin kudi sosai.

    Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari kan  yadda lamarin ke shafar rayuwar mutanen da  suke zaune a gidajen haya.

    Tue, 14 May 2024
  • 575 - Gwamnatin Zamfara Ta Sa Zare Da Ta Tarayya Kan Yaƙi Da ’Yan Bindiga

    Takaddama a tsakanin gwamantin Tarayya da ta jihar Zamfara a kan hanyar da ya kamata a bi don kawo karshen matsalar tsaro na neman yin kafar ungulu ga yunkurin kawar da barazanar ’yan bindiga.

    Gwamnatin Jihar ta Zamfara dai ta sa kafa ta shure duk wani yunkuri na sasantawa da ‘yan bindiga tana mai cewa ba da ita ba, sannan ta zargi gwamnatin Tarayya da hawa teburin shawarwari da ‘yan fashin daji ba da saninta ba.

    Ku biyo mu a Shirin Najeriya a Yau don mu duba abin da ya sa ake samun tankiya game da matsalar tsaro tsakanin gwamnatin tarayya da ta jihar Zamfara.

    Mon, 13 May 2024
  • 574 - ‘An Yafe Wa Masu PoS Biyan Harajin Yin Rijista Da CAC’

    Ga alama nan ba da dadewa ba yanayin sana’ar POS a kasar nan zai sauya. 

    Babban Bankin Najeriya (CBN) ya wajabta wa masu wannan sana’a yin rajista da Hukumar Rajistar Kamfanoni da Kungiyoyi (CAC) zuwa nan da 7 ga watan Yulin 2024.

    To amma ya batun harajin da suke korafi a kai? Ku biyo mu a Shirin Najeriya a Yau don jin matsayar CAC game da biyan kudin.

    Fri, 10 May 2024
Mostrar mais episódios