Filtrer par genre

Kasuwanci

Kasuwanci

RFI Hausa

Shirin yakan duba yadda kasuwanci da tattalin arizikin kasashen duniya ke ciki. Kana yakan ji sabbin dubaru da hanyoyin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masana’antu dangane da halin da suke ciki.

323 - Hauhawar farashin kayayyaki na ci gaba da ta'azzara a Najeriya
0:00 / 0:00
1x
  • 323 - Hauhawar farashin kayayyaki na ci gaba da ta'azzara a Najeriya

    Shirin zai maida hankali ne kan hahoton baya-bayan nan da Hukumar Kididdiga ta Najeriya ta fitar wanda ya bayyana yadda kasar ke ci gaba da fuskantar karin hauhawar farashin kayayyaki musamman na abinci, mafi muni da kasar ta gani a sama da shekaru 20. Rahoton wanda National Bureau of Statistic ta fitar a makon da ya gabata, ya cewa an fuskacin hauhawan farashin kayayyaki da sama da kashi 33 da rabi cikin 100 a watan Afrilun da ya gabata.

    Wed, 22 May 2024
  • 322 - CAC a Najeriya ta bai wa masu sana'ar POS wa'adin watanni biyu su yi ragista

    Shirin 'Kasuwa akai Miki Dole na wannan makon tare da Ahmad Abba ya maida hankali ne kan matakin gwamnatin Najeriya bukatar masu sana'ar POS da sauran masu mu'amala da na'urar da su garzawa hukumar rajistan kamfanoni ta kasar domin yin ragista kafin ranar 7 ga watan Yulin wannan shekara ta 2024.

    Wed, 15 May 2024
  • 321 - Yadda wani kamfanin kasar Denmark ya shirya zuba jarin dala biliyan 6 a Najeriya

    Shirin kasuwa akai miki dole na wannan mako ya mayar da hankali kan shirin wani kamfanin Denmark na zuba jarin kudi dala biliyan 6 a fannin tashoshin jiragen ruwan jihar Lagas ta Najeriya

    Danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Ahmad Abba

    Wed, 08 May 2024
  • 320 - Dambarwar EFCC da wasu jiga-jigan tsohuwar gwamnatin Najeriya kan badakalar kudi

    Shirin kasuwa akai miki dole tare da Ahmed Abba a wannan mako ya mayar da hankali kan matakin hukumar da ke yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annti EFCC na kaddamar na farautar tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello da kuma binciken wasu tsoffin mukarraban gwamnatin da ta shude kan cin hanci da rasha da kuma rufta da ci da dukiyar al’umma.

    A Najeriya, cikin ‘yan makonnin baya-bayan nan kusan za’a iya cewa hankulan al’ummar ƙasar sun karkata ne kan matakan da hukumar EFCC ke dauka kan wasu tsaffin jjiga-jigan gwamnatin da ta gabata, inda hukumar ta tsare kuma take shirin gurfanar da tsohon ministan sufurin jiragen saman ƙasar ƙarkashin tsohon shugaban ƙasa Mohammdu Buhari, wato Hadi Sirika, bisa zargin almundahana na ƙudi da suka kai sama da naira biliyan takwas.

    Yayin da a bangare guda, aka shiga wasan buya da cece-kuce tsakanin tsohon gwamnan jihar Kogi Alhaji Yahaya Bello da ke cewa abi umurnin kotu kan shirin kamashi yayinda shugaban hukumar ta EFCC ke cewa tabbas zai yi murabus muddun tsohon gwamnan bai gurfana don amsan laifin almundahanan sama da naira biliyan tamanin ba.

    Wadannan da wasu batutuwa da suka shafi tattalin arzikin Najeriya na kunshe a cikin wannan shiri, ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    Wed, 01 May 2024
  • 319 - Koken 'yan Najeriya na rashin saukar farashin kayan masarufi duk da faduwar Dala

    Shirin Kasuwa A Kai Miki Dole a wannan makon ya maida hankali ne kan batun korafin ‘yan Najeriya ke yi game da rashin ganin sauyi a farashin kayan amfanin yau da kullum, bayan karyewar farashin ƙudaden ƙetare masamman dalar Amurka da sanadin tashin ta ne ya haddasa mummunan tashin farashin kayayyaki a kasar, wanda har hukumar ƙididdiga ta ƙasar ta ce lamaarin ya yi muni.

    Ko da ya ke a wasu manyan biranen Najeriya irinsu Legas da Abuja, an fara ganin sauƙi a wasu kayayyakin abinci irinsu shinkafa da man girki da dai sauransu.

    Ku latsala alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba........

    Wed, 24 Apr 2024
Afficher plus d'épisodes