Filtrer par genre

Mu Zagaya Duniya

Mu Zagaya Duniya

RFI Hausa

Shirin Mu Zagaya Duniya na duba Wasu Muhimman Labarai da suka ja hankalin Duniya a cikin mako. Ana gabatar da shirin ne a ranar Asabar da safe a kuma maimaita ranar Lahadi da daddare.

448 - Gwamna Abba Yusuf ya mayar da Sarki Muhammadu Sunusi kan mukaminsa
0:00 / 0:00
1x
  • 448 - Gwamna Abba Yusuf ya mayar da Sarki Muhammadu Sunusi kan mukaminsa

    Gwamnan Kano Abba Yusuf ya rattaba hannu a wata doka  mai rusa ga baki daya masarautun Kano inda ya mayar da Sarki Muhammadu Sunusi kan mukaminsa.

    Bashir Ibrahim Idris dangane da wannan mataki ya tattauna da Abdoulkarim Ibrahim da Nura Ado Suleiman a cikin shirin Duniyar mu a yau daga nan sashen hausa na Rfi.

    Sat, 25 May 2024
  • 447 - Bitar labaran mako: Bikin cika shekaru 17 da kafuwar Sashin Hausa na RFI

    Daga cikin labarun da shirin na Muzagaya Duniya ya sake waiwaya akwai cikar Sashin Hausa na RFI shekaru 17 cif da kafuwa. Sai kuma matakin rushe sabbin masarautun da ya baiwa gwmna Abba Kabir Yusuf damar sake naɗa Sarki Muhammadu Sunusi na II a matsayin Sarkin Kano na 16.

    A Guinea kuwa, gwamnatin sojin da ke jagorantar ƙasar ce ta rufe wasu kafafen yaɗa labarai da suka hada da gidan talabijin da kuma gidajen radio da dama.

    Kotun Duniya ta baiwa Isra’ila Umarnin Dakatar da hare-haren da ta kaiwa a Rafah.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman.....

    Sat, 25 May 2024
  • 446 - Tattaunawa da Dr Kasim Garba Kurfi a shirin Duniyarmu a yau

    Wannan shiri na Duniyarmu a yau zai dinga muhawara kan harkokin yau da  kullum da ke dauke hankalin jama'a a duk ranar Asabar daga karfe 5.

    Shirin na wannan mako ya karbi bakucin Dr Kasim Garba Kurfi mai sharhi kuma masanin tattalin arziki.

    Sun, 19 May 2024
  • 445 - Mutane 15 ne suka rasa mutu sanadiyar harin da matashi ya kai Masallaci a Kano

    Daga cikin labarun da shirin wannan makon ya ƙunsa akwai harin da wani matashi a Kano ya kaiwa Masallaci ta hanyar cinna masa wuta, wadda zuwa lokacin gabatar da wannan shiri aka tabbatar da salwantar rayukan mutane 15 daga cikin akalla 30 da ke cikin Masalacin. Shirin na kuma ɗauke da tattauna wa da tsohon gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamiɗo, kan tuntubar junan da jiga-jigan jam’iyyun dawa suka fara yi a Najeriya, don kafa sabon ƙawancen da zai tunkari jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya. 

    Fira Ministan Senegal ya bayyana rashin gamsuwarsa kan wanzuwar sansanin sojojin Faransa a Ƙasar.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman.....

    Sat, 18 May 2024
  • 444 - Shirin ya duba zaben Chadi da kuma shirin ECOWAS na kafar rundunar yaki da ta'addanci

    Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Nura Ado Sulaiman

    Sat, 11 May 2024
Afficher plus d'épisodes