Filtra per genere

Muhallinka Rayuwarka

Muhallinka Rayuwarka

RFI Hausa

Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).

225 - Matsalar yoyon iskar gas yayi sanadiyyar gurbacewar ruwan sha yankin Delta
0:00 / 0:00
1x
  • 225 - Matsalar yoyon iskar gas yayi sanadiyyar gurbacewar ruwan sha yankin Delta

    Shirin na wannan mako zai yi dubi ne akan  yadda al'ummar karamar hukumar Obagi na jihar RIVERS dake yankin NIGER DELTA tarayyar Najeriya suke fama da matsalar yoyon iskar gas sanadiyar fashewar bututun da aka samu tun a watan Yunin shekarar 2023  wanda yayi sanadiyyar gurbacewar ruwan sha, wanda ya sa al'ummar ke kamuwa da cutar amai da gudawa  har zuwa wannan lokaci.

    Sat, 04 May 2024
  • 224 - Matakan da gwamnatin Najeriya ke dauka don magance matsalar tsuntsaye a gonaki

    Shirin 'Muhalli' na wannan makon tare da Nasiru Sani ya mayar da hankali ne kan tu’annatin da wasu nau'in tsuntsaye  da ake kira jan-baki ke yi wa gonaki a Najeriya tare da kokarin da gwamnati ke yi domin shawo kan lamarin.

    Sat, 20 Apr 2024
  • 223 - Yadda tsananin zafi ya ci karo da lokacin azumin watan Ramadana

    Shirin a wannan mako zai ba da hankali ne akan tsananin zafin da ake fama da shi a wasu yankuna na Nahiyar Afirka,  a wannan shekarar ya tsananta inda a wasu sassa na tarayyar Najeriya lamarin ya dan wuce misali.

    Jihar Sokoto da ke Arewacin Najeriya, jiha ce da tun asali aka sani da tsanantar kowane juyin yanayi na Zafi ko na Sanyin Hunturu ko ma na yawan saukar Ruwan sama.

    Sai a latsa alamar sauti domin sauraron shirin.

    Sun, 07 Apr 2024
  • 222 - Kaddamar da shirin inganta harkokin noma a jihar Niger

    Shirin na wanna makon zai yi dubi ne akan katafaren shirin zamanantar da aikin noma da gwamnatin jihar Nejan Najeriya ta kaddamar. Masana na ganin Jihar a matsayin wadda idan aka tattala kasar noma da take da ita, a cikinta kadai za a iya noma abincin da zai iya ciyar da kasar har ma a iya fitarwa zuwa kasashen ketare.

    A wannan aikin da aka kaddamar, gwamnatin jihar ta ce ta samar da kayan aikin fasahar noma na zamani tare da tanadar da dabarun noma daga kwararru.

    Ku latsa alamar sauti dn sauraron cikakken shirin tare da Nasiru Sani.......

    Sun, 31 Mar 2024
  • 221 - Najeriya ta kasance kan gaba a fagen noman masara a yankin yammacin Afrika

    Shirin wannan mako zai ba da hankali ne a kan yadda Najeriya ta kasance akan gaba a fagen noman masara a daukacin yankin yammacin Afrika, inda kasar ke samar da sama da kashi 48 na masarar da ake nomawa a yankin.

    Mafi yawan masarar da ake nomawa a kasar, na fitowa ne daga yankin arewacin kasar, musamman jihohin Bauchi, Kaduna, Borno, Naija da Taraba da kuma wasu ‘yan kalilan din jihohin kudu maso yammacin kasar.

    Sat, 23 Mar 2024
Mostra altri episodi