Filtra per genere

Mu Zagaya Duniya

Mu Zagaya Duniya

RFI Hausa

Shirin Mu Zagaya Duniya na duba Wasu Muhimman Labarai da suka ja hankalin Duniya a cikin mako. Ana gabatar da shirin ne a ranar Asabar da safe a kuma maimaita ranar Lahadi da daddare.

443 - Najeriya: Ƙarin albashi da gwamnati ta yi bai burge Ƙungiyar ƙwadago ba
0:00 / 0:00
1x
  • 443 - Najeriya: Ƙarin albashi da gwamnati ta yi bai burge Ƙungiyar ƙwadago ba

    Daga cikin batutuwan da shirin wannan lokaci ya waiwaya akwai, watsin da kungiyar kwadagon Najeriya ta yi da karin albashin ma’aikatan da gwamnatin kasar  ta yi.

    Sai kuma matakin Burkina faso na rufe karin kafafen yada labarai bisa rahoton da suka bayar na kisan fararen hula sama da 200 da sojoji suka yi.

    A Kenya kuwa Ambaliyar ruwan ce ta lakume rayukan mutane da dama gami da raba wasu kusan dubu 200 da muhallansu.

    Sat, 04 May 2024
  • 442 - Hukumar EFCC na neman tsohon gwamnan jihar Kogi Yahya Bello ruwa a jallo

    Daga cikin labarun da shirin karshen makon ya waiwaya akwai neman tsohon gwamnan jihar Kogi yahya Bello da hukumar EFCC ke yi ruwa a jallo, lamarin da ya kai ga daukar matakin dakile duk wani yunkurinsa na ficewa daga Najeriya

    Shirin ya kuma leƙa gabas ta tsakiya inda Iran ta ƙi fusata kan makamai masu linzamin da na’urorin tsaron sararin samaniyarta suka kakkaɓo a birnin Isfahan, waɗanda wasu majiyoyi suka ce Isra’ila ce ta yi yunkurin kai mata hari da su.

    Sat, 20 Apr 2024
  • 441 - Muhimman labarun lamurran da suka wakana a makon da ya gabata

    Masu sauraro daga sashin Hausa na RFI cikin shirin Mu Zagaya Duniya da saba zabo wasu daga cikin muhimman labarun lamurran da suka wakana a makon da ya gabata, domin bitarsu.

    A ranar Larabar da ta gabata al'ummar Musulmin Najeriya suka bi sahun takwarorinsu na duniya wajen gudanar da Sallar Idi Karama, wadda aka saba gudanarwa bayan kammala azumin watan Ramadan.

    Sat, 13 Apr 2024
  • 440 - Karin kudin wutar lantarki ya fusata 'yan Najeriya

    Shirin Mu zagaya duniya na wannan mako ya duba batun karin kudin wutar lantarki a Najeriya, halin da ake ciki a Gabas ta tsakiya da kuma rikicin siyasar Togo.

    Danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Nura Ado Sulaiman

    Sat, 06 Apr 2024
  • 439 - Bitar labaran mako: Yadda aka ceto daliban Kuriga a Kadunan Najeriya

    Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan mako tare da Rukayya Abba Kabara ya yi bitan wasu daga cikin labaran da suka fi daukar hankali a makon da ya wuce ciki har da labarin yadda gwamnatin Najeriya ta ceto daliban Kuriga da ke Jihar Kaduna tare da sada su da iyalan su.

    Akwai dambarwar da ta zagaye batun karin kudin aikin hajji da ya gigita maniyyatan Najeriyar, sai dai kuma gwamnati ta kawo dauki a wasu jihohin.Zakuji yadda harin ta’addanci mafi muni a Rasha ya hallaka mutane sama da 130, kuma tuni wadanda aka kama suka amsa laifin su.

    Sat, 30 Mar 2024
Mostra altri episodi