Podcasts by Category

Kasuwanci

Kasuwanci

RFI Hausa

Shirin yakan duba yadda kasuwanci da tattalin arizikin kasashen duniya ke ciki. Kana yakan ji sabbin dubaru da hanyoyin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masana’antu dangane da halin da suke ciki.

319 - Koken 'yan Najeriya na rashin saukar farashin kayan masarufi duk da faduwar Dala
0:00 / 0:00
1x
  • 319 - Koken 'yan Najeriya na rashin saukar farashin kayan masarufi duk da faduwar Dala

    Shirin Kasuwa A Kai Miki Dole a wannan makon ya maida hankali ne kan batun korafin ‘yan Najeriya ke yi game da rashin ganin sauyi a farashin kayan amfanin yau da kullum, bayan karyewar farashin ƙudaden ƙetare masamman dalar Amurka da sanadin tashin ta ne ya haddasa mummunan tashin farashin kayayyaki a kasar, wanda har hukumar ƙididdiga ta ƙasar ta ce lamaarin ya yi muni.

    Ko da ya ke a wasu manyan biranen Najeriya irinsu Legas da Abuja, an fara ganin sauƙi a wasu kayayyakin abinci irinsu shinkafa da man girki da dai sauransu.

    Ku latsala alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba........

    Wed, 24 Apr 2024
  • 318 - Yadda matasa suka rungumi kananan sana’o’i lokacin azumin Ramadana a Damagaram

    Shirin Kasuwa a Kai Miki Dole a wannan makon ya maida hankali ne kan kananan sana’o’i da matasa ke yi don samun na abinci a lokacin azumin watan Ramadana a Damagaram da ke jamhuriyar Nijar. wasu daga cikin sana'oin da matasan sukafi mai da hankali akai dai sun hada da bredi ko kayan marmari ko kayan lambu da dai sauransu.

    Ku latsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Ahmed Abba.......

    Wed, 03 Apr 2024
  • 317 - Gidauniyar Dangote ta kashe naira biliyan 15 na tallafin abinci a Najeriya

    Shirin Kasuwa A Kai Miki Dole a wannan makon ya maida hankali ne kan rabon tallafin abincin naira biliyan 15, da Gidauniyar Aliko Dangote ta kaddamar a Najeriya. Wannan dai na daga cikin matakan rage radadin talauci a tsakanin al'ummar Najeriya, da gidauniyyar hamshakin attajirin Afirka ta kaddamar a birnin Kano da ke arewacin kasar.

    Ku latsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Ahmed Abba.......

    Wed, 27 Mar 2024
  • 316 - Yadda matsin rayuwa ya tilastawa 'yan Najeriya fasa rumbunan abinci

    Shirin Kasuwa akai miki dole tare da Ahmed Abba a wannan makon ya yada zango ne a Tarayyar Najeriya, inda ya yi dubi kan matsanancin kuncin rayuwar da al’umman kasar suka shiga da har ta kai ana fasa rumbunan abinci ko tare manyan motocin dakon kaya a tituna ana kwasan abinci.

    Wed, 06 Mar 2024
  • 315 - Yadda al'ummar kasashen yammacin Afrika ke kokawa saboda tsadar rayuwa

    A wannan makon shirin Kasuwa akai miki dole, zai yi duba ne game da bakar ukubar da al’ummar kasashen Nahiyar Africa ke fuskanta, a sanadiyar hauhawar farashin kayayyakin masarufi, musamman kasashen Nijeriya, Nijar da kuma Cameroon. Yanzu haka dai a iya cewa wannan yanayi na hauhawar farashin kayan masarufi tuni ya zame wa kasashen Nijeriya da Nijar da Ghana da kuma Cameroon Dan zani a kasuwa.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Abdulkadir Haladu Kiyawa.....

    Wed, 28 Feb 2024
Show More Episodes