Podcasts by Category

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

RFI Hausa

Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Al’umma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalin’ariziki, al’adu da dai sauransu…

550 - Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa da dama
0:00 / 0:00
1x
  • 550 - Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa da dama

    Shirin ra'ayoyin masu saurare na wannan rana ta Juma'a ya bai wa jama'a damar tofa albarkacin bakinsu ne game da batutuwa da dama da ke ci musu tuwo a kwarya, kama daga siyasa, tattalin arziki, tsaro, zaman-takewa da dai sauransu.

    Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin.

    Fri, 26 Apr 2024
  • 549 - An fara samun karancin man fetur a sassan Najeriya

    Rahotanni daga sassan arewacin Najeriya na nuna cewar an fara samun karancin man fetur a gidajen sayar da man, abinda ya sa wasu masu man kara farashin da suke sayar da kowacce lita.

    Ko menene ya haddasa matsalar karancin man fetur din a sassan kasar?

    Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

    Thu, 25 Apr 2024
  • 548 - Kan halin rashin tsaron da arewa maso yammacin Najeriya ke ciki

    Wata kungiyar kare hakkin dan adam ta kasa da kasa da ake kira Global Rights ta bayyana cewa yankin arewa maso yammacin Najeriya shi ne mafi fuskantar ayyukan ta’addanci masu alaka da kashe-kashe ko garkuwa da mutane idan an kwatanta da yankin kudancin kasar.

    Rahoton da ya bayyana halin da ake ciki a yankin na arewa maso yammacin Najeriya da wani lamari mai tayar da hankali wanda kuma al’umma ba za su lamunci ci gaba da wanzuwarsa ba, ya ce wajibi ne mahukuntan kasar su lalubo hanyoyin warware matsalolin wannan yanki.

    Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

    Thu, 18 Apr 2024
  • 547 - An cika shekara guda da fara yakin kasar Sudan

    A farkon wannan makojn ne yakin da ake gwabzawa a Sudan tsakanin sojojin kasar karkashin Janar Abdel Fattah al-Burhan da kuma dakarun RSF da ke karkashin Mohamed Hamdan Dagalo ke cika shekara guda.

    Rikicin da aka faro a ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2023, ya yi sanadiyar rasa rayuka da dama da kuma raba miliyoyi da muhallansu, wanda a yanzu MDD ta ce akwai barazanar barkewar yunwa a kasar.

    Bangarori da dama ne dai suka yi yunkurin warware wannan rikici amma abin yaci tura.

    Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Nasiru Sani.

    Tue, 16 Apr 2024
  • 546 - Kan cika shekaru 10 da sace daliban Chibok da Boko Haram ta yi

    Yayin da aka cika shekaru 10 da sace dalibai a makarantar sakandiren 'yan mata da ke garin Chibok a jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya, har yanzu akwai matan kusan 100 da ke tsare a hannun mayakan Boko Haram da suka yi garkuwa da su.

    Gwamnatin kasar dai na ci gaba da ikirarin cewa, tana iya bakin kokarinta wajen ganin an sako sauran 'yan matan da ke hannun mayakan.

    Abin tambayar ita ce, wannen hali iyayen yara da ke hannun mayakan ke ciki?

    Yaya makomar ilimi take a Najeriya, tun daga lokacin da Boko Haram suka kafa tarihin sace dalibai kawo yanzu?

    Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

    Mon, 15 Apr 2024
Show More Episodes