Podcasts by Category

Ilimi Hasken Rayuwa

Ilimi Hasken Rayuwa

RFI Hausa

Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-daban na duniya, tare da nazari kan irin ci gaban da aka samu wajen binciken kimiya da fasaha da ke neman saukakawa Dan’adam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin irin bincike da masana ke yi domin inganta rayuwar Bil’adama. Shirin na zo maku ne, a duk ranar Talata a shirye-shiryenmu na safe, a ku maimata ranar Alhamis.

359 - Karuwar masu mallakar takardun kammala karatu na bogi a Najeriya, na barazana ga karewar kwararru
0:00 / 0:00
1x
  • 359 - Karuwar masu mallakar takardun kammala karatu na bogi a Najeriya, na barazana ga karewar kwararru

    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako ya duba yadda mallakar takardun kammala karatu na bogi a Najeriya ke barzana ga karewar kwararru a fannoni da dama.

    Ana fargabar idan har wannan dabi'a ta ci gaba a haka, tabbas za'a rasa kwararru musamman a fannin lafiya, kimiyya da sauransu.

    Danna Alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.

    Tue, 26 Mar 2024
  • 358 - An samar da cibiyar sadarwa a jahar Bauchi don saukakawa dalibai wajen bincike

    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan lokacin ya yi duba ne kan yadda wasu kungiyoyi karkashin cibiyar fasahar sadarwa da ci gaban al’umma wato CITAD suka samar da wata katafariyar cibiyar sadarwa da aka yiwa lakabi da HELLO HOPE a jahar Bauchi. Shirin ya kasance wani bangare na yunkurin saukakawa mazauna karkara hanyoyin samun sadarwa ta internet musamman wuraren da babu irin wannan ci gaba ko kuma wuraren da suke da shi amma bashi da karfi, wanda jama’are ke cikin wannan rukuni.

    Kungiyoyin da sun sha alwashin samar da irin wannan cibiyar sadarwa guda 20 a shiyoyin Najeriya shida zuwa karshen wannan shekara domin samar da internet a yankunan karkara.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna........

    Tue, 19 Mar 2024
  • 357 - Taro kan gudummawar kafafen yada labarai a bangaren tsaro a jami'ar ABU Zaria

    Matsalar tsaro na daya daga cikin matsalolin da ke addabar Najeriya, musamman ma arewacin kasar, hakan ya  sanya sashen koyon aikin jarida na jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria da ke jihar Kaduna ya shirya wani taro gagarumin taro na kasa da kasa domin tattaunawa a kan gudumawar da kafafen yada labarai za su iya bayarwa wajen warware matsalar tsaro. Ya yi wannan ne da zummar taimaka wa kokarin da al'umma ke yi wajen warware wa kansu matsalar tsaron da ke damun su.

    Tue, 05 Mar 2024
  • 356 - Yadda dalibai ke barin karatu a Nijar don tafiya neman kudi a wasu kasashe

    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan lokacin ya yi duba ne kan yadda dalibai da dama a Jamhuriyar Nijar, musaman maza ke barin karatu da sunan tafiya neman kudi, kasashen ketare kamar Libiya, Aljeriya ko kuma hako zinare a kasar Mali kai harma da kokarin tsallakawa Turai, abin da ya sanya kungiyoyin dalibai a kasar bazama aikin wayar da kan matasa kan sanin muhimmancin da ilimi ke da shi.

    A Nijar kashi 25 na yara ne ke samun zuwa makarantar boko, kuma daga yara 100 da ake sanyawa a makarantun firamare uku kadai ke kaiwa matakin jami’a.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna........

    Tue, 27 Feb 2024
  • 355 - Yadda gwamnatin jahar Neja ta fara horas da dalibai sana'oin dogaro da kai

    Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan makon zai yi duba ne kan yadda gwamnatin jahar Neja da ke Arewacin Najeriya, ta samar da shirin horas da dalibai sana'oin hannu don dogaro da kai. Gwamnatin jahar dai ta ware ranar Juma'ar kowane mako don gudanar da darasin koyon sana'oin hannu.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna........

    Tue, 20 Feb 2024
Show More Episodes