Podcasts by Category

Dandalin Siyasa

Dandalin Siyasa

RFI Hausa

Shirin Dandalin Siyasa, yana tattaunawa tare da tafka muhawar kan al’amurran siyasa da ke faruwa a kasashen duniya, da batutuwan da suka shafi al’umma kai tsaye, wanda Bashir Ibrahim Idris ke jagoranta. Wannan Shirin na zuwa ne a karshen mako Ranar Assabar da maimaci a ranar Lahadi a Shirye Shiryen Safe da Yamma.

147 - Dambarwar siyasar dakatar da Onnoghen
0:00 / 0:00
1x
  • 147 - Dambarwar siyasar dakatar da Onnoghen

    Shirin Dandalin Siyasa na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya tattauna ne kan dambarwar siyasar da ta kunno kai a Najeriya bayan shugaban kasar Muhammadu Buhari ya dakatar da alkalin alkalai, Walter Onnoghen bisa zargin sa da bayar da bayanan karya kan kudaden da ya mallaka.

    Thu, 31 Jan 2019
  • 146 - Nazari kan zaben Gwamnoni a Najeriya

    Shirin Dandalin Siyasa na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya yi nazari ne game da zabukan Gwamnoni na 'yan majalisun jihohin Najeriya da za a gudanar a ranar Asabar mai zuwa, in da ake fargabar cewa, da dama daga cikin Gwamnoni masu ci ba za su koma kan kujerunsu ba saboda wasu dalilai na siyasa.

    Thu, 07 Mar 2019
  • 145 - Shugaba Buhari ya lashe zaben Najeriya wa'adi na biyu

    Shirin Dandalin Siyasa na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya tattauna ne game da nasarar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya samu ta sake lashe kujerar shugabancin kasar wa'adi na biyu bayan doke babban abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar. Tuni Jam'iyyar PDP ta bayyana sakamakon zaben a matsayin mara inganci tana mai zargin tafka magudi a zaben,yayinda ta ce, za ta shigar da kara a kotu.

    Thu, 28 Feb 2019
  • 144 - 2019: Hankulan kasashen duniya sun karkata zuwa zabukan Najeriya

    Shirin Dandalin Siyasa na wannan mako da Bashir Ibrahim Idris ya gabatar, yayi nazari kan halin da siyasar Najeriya ke ciki, yayinda ya rage kwanaki kalilan a gudanar da zabukan kasar na 2019 a matakai daban daban. Sai kuma tsokaci da shirin ya yi kan yadda hankulan kasashen duniya ya karkata zuwa kan zabukan Najeriyar.

    Wed, 13 Feb 2019
  • 143 - Yadda Siyasa ke gudana a Jihar Kano gabanin zaben shugaban kasa

    Shirin Dandalin Siyasa na wannan makon, ya leka jihar Kano da ke tarayyar Najeriya, ida yayi nazari kan yadda al'amuran Siyasa ke gudana, yayinda ake gaf kada kuri'a a zaben shugabancin kasar na 2019 a ranar 16 ga watan Fabarairu.

    Fri, 08 Feb 2019
Show More Episodes