Podcasts by Category

Wasanni

Wasanni

RFI Hausa

A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.

579 - Nazari kan yadda wasannin kwata finals na gasar zakarun Turai su ka gudana
0:00 / 0:00
1x
  • 579 - Nazari kan yadda wasannin kwata finals na gasar zakarun Turai su ka gudana

    Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon ya maida hankali ne kan yadda wasannin matakin kwata finals na gasar zakarun Turai su ka gudana. A makon da ya gabata ne dai aka kammala wasannin zagayen, inda aka fafata a wasanni 4. Dortmund da aris Saint-Germain da Bayern Munich da Real Madrid ne suka kaiga wasan kusa da na karshe a gasar ta bana.

    A yanzu Bayern Munich zata fafata da Real Madrid ita kuwa Borussia Dortmund ta kara Paris Saint-Germain.

    Ku letsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh.......

    Mon, 22 Apr 2024
  • 578 - Hasashen yadda za ta kaya a gasar Firimiyar Ingila

    Shirin a wannan lokaci ya fi karkata akalar ne kan gasar Firimiyar Ingila, wadda ke ci gaba da jan hankali, duk da shawo gangarar da akayi.

    Yar manuniyar dai tuni ta fada kan kungiyoyin ukun saman tebur, wato Manchester City, Arsenal da Liverpool, lura da yadda suke kan kan kan a yawan maki, abunda ke kara nunawa duniya yadda gasar ta Firimiya ta ke ci gaba da jan zarenta a fagen tamola.

    Ko da yake a halin yanzu Manchester City ce ta karbe ragamar teburin wannan gasa, bayan rashin nasarar da Arsenal da kuma Liverpool suka samu a nasu wasannin.

    Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Khamsi Saleh.

    Mon, 15 Apr 2024
  • 577 - Shiri na musamman kan shirye-shiryen gasar Olympics kashi na 2

    A wannan makon Shirin Duniyar Wasanni ya yi duba ne kan yadda ake tufka da warwara game da tsarin tsaro a lokacin gasar wasannin motsa jiki ta Olympics da birnin Paris zai karbi bakunci a watan Yulin wannan shekarar.

    Shire-shiryen gudanar da gasar wasannin motsa jiki ta Olympics da birnin Paris na Faransa zai karbi bakunci a watan Yuli mai zuwa sunyi nisa, domin dai rahotanni na nuna cewar an kammala tanadin kusan dukkanin inda za a gudanar da wadannan wasanni.

    Sai dai wani hanzari ba guda ba, duk da matakan da kasar ta Faransa ta dauka na tabbatar da tsaron ‘yan wasa da kuma na ‘yan kallo, bayanai na nuna cewar akwai alamun fuskantar barazanar tsaro a lokacin gasar.

    Wannan lamari dai ya biyo bayan harin ta’addancin da aka kai birnin Moscow wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 140.

    A lokacin wata zantawa da aka yi shugaban Faransa Emmanuel Macron a makon da ya gabata, ya ce babu shakka, akwai yuwuwar Rasha za ta kai hari a lokacin gasar da ke tafe.

    Kai hari a lokacin gasar Olympics

    Kai hari a yayi gasar gujeguje da tsalle-tsalle ta Olympics a iya cewa ba sabon abu bane, domin a baya an sha samun irin hakan, wanda aka kai a shekarar 1972 a Munich da kuma a shekarar 1996 a Atlanta.

    Duk da cewa a cikin watan da ya gabata ministar Wasannin Faransa Amelie Oudea-Castera, ta ce a yanzu babu wata barazanar hare-haren ta’addanci da gasar gujeguje da tsalle-tsalle ta Olympics ke fuskanta, sai dai wasu da dama na cewa barazanar abu ne da ke da alaka da rikicin da ake gwabzawa tsakanin Rasha da Ukraine da ya kwashe sama da shekaru biyu anayi, wanda kasashen duniya ciki harda Faransa ke goyonma Ukraine baya domin fafatawa da Rasha.

    Yadda gasar Olympics ke samar da hadin kai

    Ita dai wannan gasa ana ganinta a matsayin wata farfajiya ta samar da hadin kai, ganin yadda take hada dukkanin bangarorin duniya waje guda.

    Domin idan aka koma baya cikin tarihi, bayan kawo karshen yakin duniya na biyu, gasar da aka gudanar ta shekarar 1952, ta kasance taron wasanni mafi girma a duniya da aka gudanar.

    Ƴan wasa dubu 4 da dari 955 ne suka halarci gasar daga kasashe 69, bayan maido da kasashen Japan da Jamus da wasu kasashe 13 da a karon farko ke nan suka halarci gasar, cikinsu har da Isra’ila wacce ta kasance sabuwar kasar da aka kirkira da ta samu amincewar Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 1948, da Vietnam da ke cikin rudanin siyasa.

    To sai dai ana ganin cewa a wannan karon siyasa ta shiga cikin lamarin wanda ke kokarin kawo rarrabuwar kai.

    Martanin Rasha game da zargin kai hari

    To sai dai a wani martani da Rasha ta maida game da kalaman Macron ta bakin mai magana da yawun fadar shugaban kasar Dmitry Peskov, ta ce zargin na Macron babu tushe a cikinsa kuma wani matakine na yada labaran kanzon kurege da kasashen yammaci ke yiwa Rasha.

    Mon, 08 Apr 2024
  • 576 - Sharhi game da kamun ludayin Finidi George a tawagar Super Eagles

    Shirin a wannan mako shirin ya yi sharhi ne kan kamun ludayin mai rikon kwaryar tawagar Super Eagles ta Najeriya Finidi George, bayan da tawagar ta buga wasannin sada zumunci biyu a makon daya gabata karkashin kulawar Finidi George da aka damkawa tawagar a hannunsa a matsain mai horaswa na rikon kwarya.

    Tawagar ta yi nasara kan takwararta ta Ghana a wasan farko da tayi, sai dai kuma ta sha kashi a hannun Mali karo na farko cikin gwamman shekaru da hakan ta faru.

    Ku latsa alamar sauti donjin cikakken shirin tare da Khamis Saleh......

    Mon, 01 Apr 2024
  • 575 - Masar ce ta daya a gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta Afrika da aka yi a Ghana

    Shirin Duniyar Wasanni a wannan mako yayi duba ne kan yadda gasar guje-guje da tsalle -tsalle ta nahiyar Afrika ta gudana a kasar Ghana. Kasar Masar ce ta zamo zakarar lashe lambobin yabo har 189, sai Najeriya da ke bi mata da lambobn yabo 120, yayinda Janhuriyar Nijar ta lashe lambobin yabo 11, lamarin da ya bata damar zama amatsayi na 16 a teburin kasashe 53 da suka halarci gasar bayan da Cape Verde ta janye daga fafatawa a wannan karon.

    Wannan ne kuma  karo na 13 da ake gudanar da wannan gasa a tarihi, inda aka gudanar da wasanni kusan 30.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh.....

    Mon, 25 Mar 2024
Show More Episodes